Posts

Showing posts from August 13, 2021

RADDI ZUWA GA AISHA YESUFU BAYAHUDIYA A RIGAR MUSULUNCI Kamfanin jaridar Legit sun tattauna da bayahudiya a rigar Aisha Yesufu fitacciyar 'yar gwagwarmayar kare dabi'un yahudanci a Nigeria, inda a cikin tattaunawar tace wai Datti Assalafiy da Sheikh Alkasim Asadul Islam mun fitar da mijinta daga Musulunci kamar yadda jaridar ta ruwaitoAisha Yesufu tace wai ana tsangwamarta akan cewa ta cire hijabi, saboda abinda takeyi a cikin Hijabi bai dace da dabi'un Musulmai ba, ita kuma ta hakikance akan cewa ita Musulma ce da mijintaTabbas akwai gurin da na taba rubutu nace mijin Aisha Yesufu ba Musulmi bane, sannan ita ma nace ina da shakku akan Musuluncinta, wannan maganar da na fada ina da madogara kamar haka:Kafin wutar zanga-zangar ENDSARS ta mutu, ranar 15-11-2020 da misalin karfe 4 na yammaci, Aisha Yesufu ta wallafa sako a shafinta na Twitter tace: "mijinta ya shiga cikin damuwa sosai, saboda an saka Limamin addininsu na Nasara Pastor Sam Adeyemi cikin wadanda aka zargi, bai sani ba nima sunana ya shiga cikin wadanda ake zargi, mijina yana ta mamakin yadda aka saka sunan Limaminsa.." inji Aisha YesufuWannan dalilin ya isa zama hujja ga kowa ya iya fahimtar addinin Mijin wannan bayahudiya a rigar Musulunci kamar yadda zaku ga hoton screenshot yadda ta rubuta da turanci a shafinta na TwitterBabu Musulunci a gurin Aisha imbanda Hijabin da take sakawa, Aisha tana da dabi'u sak irin na 'yan bazata, wakilan yahudawa makiya addinin Musulunci da suke zuwa kasashen larabawa suna koyon Musulunci su boye kafurci su dawo su shiga cikin Musulmi su gurbatasuDaga cikin dalilan da yasa muke da shakku akan Musuluncin Aisha shine yadda ta fito baro-baro a shafinta na Twitter ta kalubalanci Gwamnatin Nigeria akan haramcin auren 'yan Luwadi da Madigo, Aisha Yusuf tace ya zama dole a bawa 'yan Luwadi da Madigo 'yanci, anya Musulma irin wannan a cikin Hijabi zata goyi bayan Luwadi da Madigo?Wai shin ya dace a kalli Musulma cikin masu neman a bada 'yan cin auren 'yan Luwadi da Madigo a matsayin Musulma?, ko a cikin kafurai da suke goyon bayan Luwadi sai rubabbuDaga cikin dalilan da yasa muke da hujjar kokwanto akan Musuluncin Aisha shine, duk inda arna suka fito suna yakar Musulunci tana goyon bayansu, kadiyyar da ta faru da Malam Sheikh Dr Isa Ali Pantami, makiya Musulunci suka masa sharri cewa yana goyon bayan ta'addanci, cikin wadanda suka fito sukayi kira da a cireshi daga mukamin Minista har da ita wannan bayahudiya a rigar Musulunci, Allah ya 'Daga Muslinci

Image

LABARI DA DUMI DUMINSA AN GARZAYA DA GWAMNA NASEER EL-RUFA'I KASAR WAJE DOMIN NEMAN LAFIYA .DAGA MURYAR YANCI .Ruhotannin da suke shigo mana daga majiyar mu ta fadar gwamnatin Jihar Kaduna ya tabbatar mana da cewa Mai girma gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir Ahmed El Rufa’i na kwance a wani asibitin ketare ana duba lafiyarsa .Majiyar mu daya bukaci a sakaya sunansa yace ko a shekaranjiya laraba da shugaban dakarun sojin kasan Najeriya General Yahaya Bello yazo Kaduna ziyarar aiki na musamman akan sha’anin tsaro amma bai samu damar ganawa da gwamnan ba, sai dai yayi wa mataimakiyar gwamna Hajiya Hadiza Balarabe wanda a yanzu ita ke jan ragamar Jihar Kaduna kamin El Rufa’i ya dawo, inda shugaban dakarun sojin yai mata bayanin zuwansa Kaduna.Duk da dai majiyar mu bai San wani irin ciwo bane yasa aka kai gwamnan asibitin ketare,Amma wakilin mu ya tuntubi Mai taimakawa gwamnan akan sha’anin watsa labarai, Mallam Ibrahim Amma haryanzu da muke rubuta wannan rahoton bai kira yayi mana karin haske ba Kuma bai aiko mana Koda amsar sakon karta kwana da muka tura mai ba.Zamu kawo maku cikakken rahoton yadda lamarin yake da zarar mun samu sahihin Bayani daga makusanta gwamnan.Allah ya bashi lafiya da dukkan marasa lafiya dake gida da asibiti AminRahoton Muryar 'Yanci

Image