Posts
Showing posts from August 12, 2021
KWAMITIN ZAGAYEN MAULUDIN MANZON TSIRA (S.A.W.W) YA KAI GUDUN MAWAR MAGANI A ASIBITIN FUNTIWA. DAGA HUSSAINI YERO FUNTUA.Kwamitin zagayan Maulidin Annabi (SAW ) karkashi jawuyar Shek Abubukar Alti Funtuwa,su kai tallafin magani a Asibitin Tundun wada Funtuwa dan talawa masu Annobar Gudawa da Mai. Shugaban Kwamitin Lafiya na Zagayan Maulidin Malam Hafizu Tukur da Sakataren babban Kwami Zartarwar Kamitin , Ibrahim Bawa da saura Manbonin suka jagoranci mika tallafin magani ga Shugaban Asibitin Tundun .A jawabin sa Malam Hafizu Tukur ya bayyana cewa, Kwamitin zagayan Maulidin na Yan Funtua da Zawuyar Shek Abubukar Alti ke gudanarwa a duk shekara, qarqashin jagorancin Khalifa Ali Saidu Alti ,muka kawo ma 'yan uwan mu da Annobar Gudawa da Mai ya same su.albarkacin Sayyidina Rasulillahi (swa) .da fatan Allah ya masu lafiya ya Kuma kawo mana karshen wannan Annoba.A nasa jawabin , Sakataren Kwamatin Amadadin Shugaban Babban Kwamitin, Bishir Muhammad Kin Funtuwa ya bayyana cewa,Wannan Kwamitin zagayan Maulidin yana gudanar da ayyukan jinkan da tallafawa Marasa karfi da ziyar gidan Yari da da dai sauran su.Shugaba Mai kula da Asibitin Tundun wada Funtuwa,Lawal Shehu Auta (Lawal ta) ,ya bayyana godiyar sa ga Kwamitin zagayan Maulidin Annabi da ya kawo mana gudunmuwar magunguna Kuma Wannan tallafin yazo alokacin da ya dace,Kuma zai taimaka wajan ceton rayuwar mutane da dama.Kuma yayi kira ga sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni da suyi koyi da Wannan Kwamitin zagayan Maulidin Annabi dan talafawa marasa lafiya Gudawa da Mai.
- Get link
- X
- Other Apps
NAR TV
CARGO TV